Ɗan takarar gwamnan jihar Sokoto a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, Hon. Manir Muhammad Dan’Iya, ya yi Allah-wadai da zargin riƙe albashin malaman makarantu da sauran ma’aikatan ƙananan hukumomi saboda goyon bayan jam’iyyar ADC.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Aminu Abdullahi ya fitar, Dan’Iya ya bayyana zargin a matsayin danniya da nuna wariya, yana mai cewa bai kamata gwamnati ta yi amfani da albashin ma’aikata ko cibiyoyin gwamnati wajen tsoratar da mutanen da ke goyon bayan jam’iyyun adawa ba.
Dan’Iya ya ce ma’aikata na da haƙƙin samun albashin da suka yi aiki suka cancanta, tare da ’yancin zaɓar jam’iyyar da suke so ba tare da fargabar hukunci ko takura ba.
Ya bayyana damuwarsa kan wani bayani da ya ce ya samu, wanda ke zargin cewa an gudanar da wani taro a harabar hukumar kula da ilimin firamare, inda ake zargin wasu jami’ai sun amince da ci gaba da riƙe albashin malaman da ake ganin suna goyon bayan ADC na tsawon wasu watanni uku.
Sanarwar ta ƙara da cewa ana zargin an tsara ci gaba da wannan mataki har zuwa bayan zaɓe, sannan a yanke shawarar abin da zai biyo baya bisa sakamakon zaɓen.
Dan’Iya ya buƙaci gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, da hukumomin da abin ya shafa su fito fili su bayyana matsayarsu kan zargin, tare da tabbatar da cewa ba a hana wani ma’aikaci albashin da ya cancanta saboda ra’ayinsa na siyasa ba.
Ya ce albashin ma’aikaci haƙƙinsa ne da ya samu ta hanyar gudanar da aiki, ba wata kyauta ba ce da za a iya bayarwa ko ƙwacewa bisa biyayya ga wata jam’iyya.
Dan’Iya ya kuma bayyana damuwa kan rahotannin da ke zargin cewa wasu jami’an gwamnati da abokan hulɗarsu na lalata ko cire allunan tallan ADC da fastocinta a wasu wurare.
Ya yi Allah-wadai da irin waɗannan ayyuka idan aka tabbatar da su, yana mai cewa ya kamata a bar kayan yaƙin neman zaɓen ADC su kasance tare da na APC da sauran jam’iyyun siyasa cikin zaman lafiya, matuƙar ana bin ƙa’idojin da doka ta tanada.
Ɗan takarar ya tunatar da gwamnatin jihar cewa kundin tsarin mulkin Nijeriya ya tanadi ’yancin faɗar albarkacin baki, haɗuwa da sauran mutane da kuma shiga harkokin siyasa bisa doka.
Ya ce yaƙin neman zaɓensa zai riƙa tattara bayanai kan duk wani rahoton hana biyan albashi, tsoratar da ma’aikata ko lalata kayan kamfen, tare da ɗaukar matakan shari’a idan hujjoji suka tabbatar da zarge-zargen.
Dan’Iya ya kuma yi kira ga hukumomin kula da ma’aikata, hukumomin kare haƙƙin ɗan Adam, jami’an tsaro da hukumomin zaɓe da su binciki ƙorafe-ƙorafen, tare da ɗaukar matakan da suka dace bisa ikon kowace hukuma.
