DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Thursday, October 15, 2026
HomeLabaraiMagoya bayan Pantami sun gudanar da addu'o'i don neman samun nasara

Magoya bayan Pantami sun gudanar da addu’o’i don neman samun nasara

Magoya bayan tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani na Nijeriya, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, sun gudanar da addu’o’i na musamman domin neman taimakon Allah, bayan hukumar zaben Nijeriya (INEC) ta cire sunansa daga jerin sunayen ƙarshe na ’yan takarar gwamnan jihar Gombe.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa magoya bayan Pantami sun taru ne a ranar Laraba a harabar makarantar Government Comprehensive Day Secondary School da ke cikin birnin Gombe, inda suka gudanar da addu’o’in neman taimakon Allah kan abin da suka bayyana a matsayin cire shi daga takara bisa dalilan siyasa.

A yayin addu’o’in, magoya bayan sun roƙi Allah ya tabbatar da adalci tare da dawo da Pantami a matsayin ɗan takarar jam’iyyar PDP na kujerar gwamnan jihar Gombe.

Sun kuma roƙi Allah ya kare tsohon ministan daga dukkan sharri, tare da ba shi nasara a harkokin siyasar da yake gudanarwa.

Ɗaya daga cikin magoya bayan, Ahmed Sani, ya ce sun shirya addu’o’in ne domin neman taimakon Allah, baya ga matakan shari’a da na siyasa da suke ɗauka domin warware matsalar.

Ahmed ya ce sun yi duk abin da ya kamata ta fuskar siyasa da shari’a, kuma a yanzu sun miƙa lamarin ga Allah, suna fatan a yi musu adalci.

Ya bayyana Pantami a matsayin wanda suke ganin zai iya wakiltar muradun al’ummar Gombe, yana mai cewa suna da yakinin cewa za a tabbatar da adalci a ƙarshe.

Shi ma wani magoyin bayan Pantami, Ibrahim Mohammed, ya ce duk da ƙalubalen da tsohon ministan ke fuskanta, sun yanke shawarar gudanar da addu’o’i na musamman domin samun nasarar shari’ar da ake yi kan batun takararsa.

INEC ta fitar da jerin ƙarshe na ’yan takarar a ranar 10 ga Oktoba, 2026, amma ba a saka sunan Pantami a ciki ba.

Bayan wannan mataki, lauyoyin Pantami sun bayyana cire sunansa a matsayin abin da bai dace da doka ba, tare da bai wa INEC wa’adin kwanaki uku domin wallafa sunansa.

Sai dai INEC ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata cewa cire sunan Pantami da na wasu ’yan takara daga jerin ya samo asali ne daga rashin bin tanade-tanaden sashe na 77 na dokar zaɓe ta shekarar 2026.

Batun ya jawo sabani tsakanin ɓangaren Pantami da hukumar zaɓe, yayin da magoya bayansa ke ci gaba da neman a warware matsalar ta hanyar addu’o’i da kuma matakan shari’a.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata