DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeKetareFarashin kayayyaki a Birtaniya ya ragu zuwa kashi 2.6 cikin 100 a...

Farashin kayayyaki a Birtaniya ya ragu zuwa kashi 2.6 cikin 100 a watan Yuni

Adadin hauhawar farashin kayayyaki a Birtaniya ya ragu fiye da yadda masana tattalin arziƙi suka yi hasashe, inda ya koma kashi 2.6 cikin 100 a watan Yuni daga kashi 2.8 cikin 100 da aka samu a watan Mayu.

Ofishin Kididdiga na kasar Birtaniya (ONS) ya bayyana cewa raguwar farashin man fetur da dizal na daga cikin manyan dalilan da suka sa hauhawar farashin kayayyaki ya ragu.

Masana sun yi hasashen cewa hauhawar farashin zai ragu zuwa kashi 2.7 cikin 100 ne kawai, amma alkaluman da aka fitar sun nuna ya koma kashi 2.6 cikin 100.

Sai dai masana tattalin arziƙi sun yi gargadin cewa raguwar na iya zama na ɗan lokaci, sakamakon tashin farashin man fetur da ake sa ran zai biyo bayan sabon rikici a Gabas ta Tsakiya.

Sabon Firaministan Birtaniya, Andy Burnham, ya yi alkawarin rage matsin tattalin arziƙin da jama’a ke fuskanta, musamman ta hanyar rage nauyin tsadar rayuwa.

Hakazalika, sabon Ministan Kuɗi, John Healey, ya ce raguwar hauhawar farashin labari ne mai daɗi ga iyalai, amma har yanzu akwai sauran aiki da gwamnati ke bukatar yi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata