Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Nijeriya (FRSC) reshen jihar Kano ta ce za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta hana jami’anta gudanar da aiki a kan titunan gwamnatin jihar da na ƙananan hukumomi.
Hukuncin, wanda Mai Shari’a M. S. Shuaibu ya yanke, ya taƙaita ikon FRSC a Kano zuwa manyan hanyoyin gwamnatin tarayya kaɗai.
Kotun ta yanke hukuncin ne bayan Barrista Abba Hikima ya shigar da ƙara, yana zargin jami’an FRSC da kafa shingayen bincike a titunan cikin birnin Kano ba tare da hujjar karya dokar hanya ba.
Mai shari’ar ya ce hakan ya saɓa wa dokar kafa FRSC tare da tauye haƙƙin ’yan ƙasa na walwala da kuma ’yancin zirga-zirga da kundin tsarin mulkin Nijeriya ya tanada.
Kotun ta kuma umarci FRSC da ta daina aiki a kan hanyoyin jiha da na ƙananan hukumomi a Kano, ta buga takardar neman afuwa a wata jarida ta ƙasa, sannan ta biya diyyar naira dubu 800.
Da yake mayar da martani, Kakakin FRSC a Kano, CRC Abdullahi Aliyu Labaran, ya ce hukumar na mutunta hukuncin kotu, amma tana ganin an yi kuskuren fassara hukuncin a tsakanin jama’a.
Ya bayyana cewa hukuncin bai soke ikon FRSC da dokar kafa ta ba, sai dai ya taƙaita ayyukanta a Kano zuwa hanyoyin gwamnatin tarayya.
Ya ce hanyoyin da FRSC za ta ci gaba da aiki a kansu sun haɗa da hanyar Kano zuwa Zariya, Kano zuwa Katsina, Kano zuwa Maiduguri, Kano Western Bypass, Airport Road da Murtala Mohammed Way.
FRSC ta kuma nuna damuwa kan saƙonnin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ƙarfafa direbobi su ƙi bin umarnin jami’anta, tana mai gargadin cewa hakan na iya haifar da rikici da kuma jefa rayuka cikin haɗari.
Hukumar ta ce za ta ci gaba da gudanar da aikinta bisa doka a manyan hanyoyin gwamnatin tarayya yayin da take jiran sakamakon ƙarar da za ta ɗaukaka, tare da kira ga masu ababen hawa da su cigaba da ba jami’anta haɗin kai.
