- Ƙungiyar dillalan man fetur ta Nijeriya (IPMAN) ta ce gidajen mai da ke Abuja da kewaye za su fara rage farashin fetur a cikin ’yan kwanaki masu zuwa, da zarar sabbin kayayyakin man fetur sun fara shigowa kasuwa.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito sakataren yaɗa labaran ƙungiyar na ƙasa Chinedu Ukadike, ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labaran Nijeriya (NAN) ranar Alhamis a Abuja.
Ukadike ya ce dillalan man fetur na shirin sake duba farashinsu da dabarun sayar da man da zarar sabbin kayayyakin sun fara shigowa kasuwa, yana mai cewa hakan na iya kawo sauye-sauye a kasuwar.
Ya ce har yanzu ba a tabbatar da takamaiman ranar da sabbin kayayyakin za su fara shigowa kasuwa ba, amma da zarar an fara shigo da su, dillalan za su gaggauta daidaita farashin tare da samar da kayayyakin ga masu amfani.
A cewarsa, sayen sabbin kayayyakin na iya fara isowa kasuwanni cikin ’yan kwanakin nan, gwargwadon lokacin da tsarin zai fara aiki, kuma dukkan matakan za su kasance bisa ƙa’idoji da dokokin da ake da su.
Rahoton NAN ya ce matakin na zuwa ne bayan matatar Dangote ta ƙara farashin man fetur daga N1,165 kan kowace lita zuwa N1,185, sannan zuwa N1,200 da N1,265 cikin mako guda, lamarin da ya jawo tashin farashin a gidajen mai da ke Abuja.
Wancan mataki dai ya jawo damuwa tsakanin masu ababen hawa, waɗanda suka yi kira ga Gwamnatin Tinubu ta ɗauki matakan gaggawa domin daidaita farashin fetur, yayin da IPMAN ke cewa ana sa ran farashin zai sauya bayan sabbin kayayyakin sun fara shigowa kasuwa.
