Ƙungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta fara binciken ladabtarwa kan ɗan wasanta, Raul Asencio, bayan an same shi da laifin tuƙin mota cikin maye a watan Agusta.
Jaridar Punch ta mai horaswar kungiyar, José Mourinho, ya bayyana hakan ranar Alhamis, inda ya ce Asencio mai shekaru 23 ya wuce adadin barasa da doka ta amince da shi da fiye da sau uku a lokacin da lamarin ya faru ranar 16 ga Agusta.
Kotun San Bartolomé de Tirajana da ke Gran Canaria ta same shi da laifi, inda ta ci tararsa €14,400 tare da dakatar da lasisin tukinsa na tsawon watanni takwas.
Bugu da ƙari, Asencio na fuskantar wata shari’a a Gran Canaria kan zargin yada wani bidiyon lalata ba tare da yardar wadanda abin ya shafa ba, wanda ake zargin an dauka tun shekarar 2023. Tsoffin ’yan wasan Real Madrid uku su ma suna fuskantar shari’ar da ta shafi wannan batu.
Mourinho ya ce duk da cewa Asencio kwararre ne kuma yana nuna ƙwazo wajen atisaye, ɗan wasan Real Madrid yana wakiltar kungiyar a kowane lokaci, ciki har da abin da yake aikatawa a wajen fili.
An kuma ruwaito ya ce duk abin da wani ɗan wasa ke yi a wajen fili yana wakiltar Real Madrid kuma zai iya shafar martabar kungiyar da kimarta a idon jama’a.
Mourinho, ya kuma ce ba ya farin ciki da abubuwan da suka faru, duk da cewa ya amince kowa na iya yin kuskure.
Asencio, wanda ya samu rauni a tsokarsa a watan Yuli, bai samu shiga cikin tawagar Real Madrid da za ta buga wasa ba tun bayan zuwan Mourinho, duk da cewa ya kasance cikin ’yan wasan da kungiyar ta rika amfani da su akai-akai a kakar wasanni biyu da suka gabata.
