Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya musanta zargin cewa an yi ma shi tayin Naira biliyan 500 domin ya kara ya kara da ɗan takarar shugaban ƙasa NDC Peter Obi, da nufin raba ƙuri’un yankin Kudu maso Kudu.
Mai baiwa Jonathan Shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Ikechukwu Eze, a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja, ya bayyana rahoton a matsayin ƙarya tsagwaronta kuma marar tushe.
Eze ya buƙaci ƴan Najeriya da su yi watsi da abin da ya kira rahoton ƙage da wani shafin yanar gizo ya wallafa, inda ya yi iƙirarin cewa an ba Jonathan kuɗi domin ya shiga takarar shugaban ƙasa.
