Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kafa kwamiti na musamman kan yaki da shan miyagun kwayoyi da safarar su, a wani mataki na kara karfafa yaki da matsalar shaye-shaye da laifukan da ke da alaka da miyagun kwayoyi a jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Darakta yada labarai na gidan Gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Alhamis.
Sanarwar ta bayyana cewa an nada tsohon Shugaban hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Barrista Muhuyi Magaji Rimingado, a matsayin shugaban kwamitin.
Sauran mambobin kwamitin sun hada da Alhaji A.A. Zaura, Kwamandan NDLEA, wakilan ma’aikatar lafiya, DSS, Rundunar ‘yan sanda, NSCDC, hukumar Kwastam, hukumar shige da fice, hukumar Hisbah, majalisar masarautar Kano, majalisar Malamai da sauran masu ruwa da tsaki.
An kafa kwamitin ne domin samar da hadin gwiwar hukumomi daban-daban wajen dakile hanyoyin safarar miyagun kwayoyi, gaggauta gurfanar da masu laifi a gaban kotu da kuma rage yawan masu amfani da miyagun kwayoyi ta hanyar fadakarwa da wayar da kai.
Daga cikin ayyukan da aka dorawa kwamitin akwai tattara bayanan sirri da musayar bayanai tsakanin hukumomin tsaro, gano da tarwatsa kungiyoyin safarar miyagun kwayoyi, da kuma samar da hanyoyin sirri da jama’a za su rika bayar da bayanai.
Kazalika, kwamitin zai gano manyan wuraren da ake rarraba miyagun kwayoyi a fadin jihar, ya taimaka wajen gudanar da samame da kama masu laifi tare da bayar da shawarwari kan kwace kadarorin da aka samu ta hanyar safarar miyagun kwayoyi.
An kuma dora wa kwamitin nauyin samar da hanyoyin da za su tabbatar da saurin gurfanar da wadanda ake zargi ta hanyar tattara hujjoji yadda ya kamata, amfani da binciken kimiyya da kuma hadin gwiwa da bangaren shari’a domin samar da kotuna na musamman da za su rika sauraron irin wadannan shari’u cikin gaggawa.
A bangaren wayar da kai kuwa, kwamitin zai jagoranci shirye-shiryen fadakarwa ga dalibai, matasa da sauran rukunin jama’a masu hadarin fadawa cikin shaye-shaye, tare da hada kai da malamai da sarakuna wajen yakar matsalar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa shan miyagun kwayoyi na daga cikin manyan barazanar da ke fuskantar makomar matasan Kano, yana mai jaddada kudirin gwamnatinsa na amfani da dukkan hanyoyin da suka dace wajen magance matsalar.
Ya bukaci mambobin kwamitin da su gudanar da ayyukansu cikin gaskiya, kwarewa da kishin kasa domin kare makomar matasa da ci gaban Jihar Kano.
