DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeLabaraiTu'ammali da miyagun kwayoyi na bayar da gudunmawa kan matsalolin tsaro a...

Tu’ammali da miyagun kwayoyi na bayar da gudunmawa kan matsalolin tsaro a Sokoto – Gwamna Ahmed Aliyu

Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya bayyana cewa tu’ammali da miyagun kwayoyi na da alhakin kusan kashi 80 cikin 100 na matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta, yana mai bayyana matsalar a matsayin babbar barazana ga makomar matasa da ci gaban al’umma.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin wani taron lacca da aka shirya domin tunawa da ranar yaki da shan miyagun kwayoyi da safararsu da Majalisar Dinkin Duniya ta twa ware na shekarar 2026, wanda aka gudanar a cibiyar Sultan Maccido Institute for Qur’an and General Studies da ke Sokoto.

Da yake jawabi ta bakin mataimakinsa, Alhaji Idris Mohammed Gobir, gwamnan ya ce mafi yawan masu aikata laifukan ta’addanci da garkuwa da mutane suna aikata hakan ne bayan sun sha kwayoyin da ke sa mayen.

“Matsalolin tsaron da ke addabar jiharmu, kashi 80 cikin 100 suna da alaka da amfani da miyagun kwayoyi, wadannan mutane suna amfani da munanan kwayoyi masu sa maye, mutum mai cikakken hankali ba zai kalli dan uwansa ya kashe shi ba,” in ji shi.

Ya ce shan miyagun kwayoyi na lalata rayuwar iyalai, hana matasa cimma burinsu, da kuma kara yawaitar laifuka da matsalolin lafiya da zamantakewa a cikin al’umma.

Gwamna Aliyu ya bukaci matasa su nisanci shaye-shaye domin su samu damar zama shugabanni, ministoci, gwamnoni da manyan jami’an gwamnati a nan gaba, yana mai cewa hakan ba zai yiwu ba idan suka fada cikin harkar kwayoyi ko safararsu.

Ya kuma nuna damuwa kan yadda safarar miyagun kwayoyi ke kara karfi, yana mai cewa hakan na taimakawa kungiyoyin masu aikata manyan laifuka tare da barazana ga tsaron kasa da na duniya baki daya.

A cewarsa, yawancin ‘yan bindiga da sauran masu aikata munanan laifuka suna aikata ta’addanci ne saboda tasirin miyagun kwayoyi, lamarin da ke sa su kashe mutane da kona kauyuka ba tare da nuna tausayi ba.

Gwamnan ya jaddada cewa yaki da matsalar shaye-shaye ba aikin hukumomin tsaro kadai ba ne, yana mai kira ga iyaye, malamai, sarakuna, kungiyoyin farar hula, kwararrun ma’aikatan lafiya da kafafen yada labarai da su hada hannu wajen magance matsalar.

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta kafa Ofishin babban mataimaki na musamman kan kula da yaki da shan miyagun kwayoyi domin jagorantar shirye-shiryen wayar da kai da hada kai da masu ruwa da tsaki wajen yakar matsalar a fadin jihar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata