Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya rattaba hannu kan dokar kasafin kuɗin shekarar 2026 wadda ta kai jimillar Naira tiriliyan 68.32, tare da kuma amincewa da tsawaita aiwatar da kasafin 2025 zuwa ranar 30 ga Yunin, 2026.
Wata sanarwa daga fadar shugaban, ta ce sabon kasafin ya ware Naira tiriliyan 4.799 domin biyan kudaden da doka ta tanada, yayin da aka keɓe tiriliyan 15.8 domin biyan bashin gwamnati, wanda ke nuna yadda bashin ke ci gaba da ɗaukar kaso mai tsoka a kasafin ƙasar.
Haka kuma, an ware naira tiriliyan 15.4 domin kashe kuɗaɗen gudanarwa, yayin da aka ware tiriliyan 32.2 domin ayyukan raya ƙasa (capital projects), wanda ya kai kusan kashi 50 cikin 100 na dukkan kasafin.
Gwamnatin ta bayyana cewa wannan tsari na nuna aniyar ta wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki, tsaro, gina ababen more rayuwa da kuma bunƙasa ci gaban al’umma baki ɗaya.
A lokaci guda, shugaban ya kuma sanya hannu kan kudirin gyara dokar kasafin 2025, wanda ya tsawaita wa’adin aiwatar da bangaren ayyukan raya ƙasa daga Maris 31 zuwa Yuni 30, 2026.
A cewar gwamnatin, wannan tsawaitawa zai bai wa ma’aikatu da hukumomin gwamnati damar kammala ayyukan da suka kusa ƙarewa, musamman manyan ayyukan more rayuwa da ke gudana a sassa daban-daban na ƙasar.
