An shigar da ƙara a kotu kan majalisar dokokin jihar Kano, inda ake neman a hana ta tantance Murtala Sule Garo a matsayin mataimakin Gwamnan jihar.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa masu ƙarar sun roƙi kotun da ta dakatar da duk wani shiri na tantancewar har sai an kammala sauraron ƙarar da ke gabanta.
Lauyoyin masu ƙarar sun bayyana cewa batun na gaban kotu ne, don haka bai dace majalisar ta ci gaba da wani mataki ba kafin a yanke hukunci, tare da jaddada cewa ci gaba da tantancewar na iya kawo cikas ga tsarin shari’a tare da saba ka’idojin doka.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara kan nadin Garo, wanda ake shirin maye gurbin mataimakin Gwamna a jihar Kano.
Lamarin na kara nuna yadda siyasar Kano ke kara daukar sabon salo, inda batutuwan doka ke taka muhimmiyar rawa wajen yanke hukunci kan manyan mukamai.
Har yanzu dai ana jiran matakin kotu kan wannan ƙara, wanda zai tantance ko majalisar za ta ci gaba da aikin tantancewar ko kuma za a dakatar da shi.
