Gwamnatin jihar Bauchi ta umurci dukkan masu rike da mukaman siyasa da ke da niyyar tsayawa takara a zabukan fidda gwani da ke tafe da su yi murabus kafin ranar Juma’a, 24 ga Afrilu, 2026.
A wata sanarwa da mai ba gwamnan jihar shawara kan harkokin yada labarai, Mukhtar Gidado ya fitar, ta ce wannan mataki ya dace da dokar zabe ta 2026, domin tabbatar da bin doka da oda a harkokin zabe.
Sanarwar ta kara da cewa gwamnatin ta yaba wa irin gudunmawar da wadannan mutane suka bayar wajen ci gaban jihar, tare da yi musu fatan alheri a kokarinsu na na shiga zaɓe
Haka kuma, an umarce su da su mika dukkan kadarorin gwamnati da ke hannunsu tare da ayyukansu ga wadanda suka dace a ma’aikatunsu kafin barin aikin nasu.
