DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, October 5, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Nijeriya ta ayyana Alhamis a matsayin ranar hutu domin bikin samun...

Gwamnatin Nijeriya ta ayyana Alhamis a matsayin ranar hutu domin bikin samun ’yancin kai

Gwamnatin Nijeriya ta ce Alhamis, 1 ga Oktoba, 2026, ranar hutu ce domin bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kan Nijeriya.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin kasar, cikin wata sanarwa da babbar sakatariyar ma’aikatar, Magdalene Ajani ta sanya wa hannu a ranar Laraba.

Ministan ya taya ’yan Nijeriya da ke cikin gida da waɗanda ke ƙasashen waje murnar zagayowar ranar samun ’yancin kan ƙasar.

Ya buƙaci ’yan Nijeriya su yi amfani da wannan dama wajen nuna haɗin kai, kishin ƙasa, zaman lafiya da mutunta juna, tare da tunawa da muhimmancin haɗin kan ƙasa.

Tunji-Ojo ya ce zaman lafiya da kwanciyar hankali muhimman abubuwa ne da ake buƙata domin samun ci gaban ƙasa mai ɗorewa.

Ya kuma yi kira ga ’yan Nijeriya su yi koyi da waɗanda suka kafa ƙasar, musamman wajen nuna ƙauna da kishin Nijeriya da kuma fifita abin da ya shafi ci gaban ƙasa.

Ministan ya bayyana cewa duk da ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta, akwai fata na samun kyakkyawar makoma, yana mai cewa bambancin al’ummar Nijeriya na daga cikin abubuwan da za su iya ƙarfafa ƙasar idan aka yi amfani da shi yadda ya kamata.

A cewarsa, haɗin kan ’yan Nijeriya da ƙudurin gina ƙasa mai ƙarfi su ne ginshiƙan da za su taimaka wajen samar da Nijeriya mai wadata da ci gaba.

Ya kuma tabbatar wa ’yan ƙasar cewa Gwamnatin Tarayya na ci gaba da ɗaukar matakan ƙarfafa tsaron ƙasa da inganta lafiyar jama’a.

Tunji-Ojo ya ce gwamnati na kuma ƙoƙarin samar da yanayin da zai bai wa ’yan Nijeriya damar rayuwa, yin aiki da kuma gudanar da harkokinsu na halal cikin kwanciyar hankali da ƙarfin gwiwa.

Ministan ya ƙara da cewa shirin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wato Renewed Hope Agenda, zai ci gaba da mayar da hankali wajen samar da ingantacciyar Nijeriya ga dukkan ’yan ƙasa.

Ya sake kira ga al’ummar ƙasar da su yi amfani da bikin ranar ’yancin kai wajen sabunta jajircewarsu ga haɗin kan ƙasa da zaman lafiya tsakanin al’ummomi daban-daban.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata