DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, July 8, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Sakkwato ta ware Naira biliyan 1.65 domin sayen taki da iri...

Gwamnatin Sakkwato ta ware Naira biliyan 1.65 domin sayen taki da iri ga manoma

Gwamnatin jihar Sakkwato ta amince da kashe Naira biliyan 1.65 wajen sayen takin zamani da ingantattun iri da magungunan noma domin tallafa wa manoma a daminar bana.

Wannan na ƙunshe ne a cikin bayanan taron Majalisar Zartarwar Jihar da aka gudanar a Fadar Gwamnatin Sakkwato, kamar yadda Darakta Janar na Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Abubakar Bawa, ya bayyana.

Majalisar ta kuma amince da sayen babura 1,200 na Daylong kan sama da Naira biliyan 1.6, waɗanda za a bai wa ma’aikatan gwamnati ta hanyar tsarin rance, kamar yadda Gwamna Ahmad Aliyu ya yi alkawari a bikin Ranar Ma’aikata.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata