Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Dokta Bukola Saraki, ya ce ’yancin cin gashin kan majalisa na da matuƙar muhimmanci ga dorewar dimokuraɗiyya a Nijeriya.
Saraki ya bayyana haka ne yayin wani taron lacca na ranar 12 ga Yuni da ƙungiyar Covenant Nation ta shirya, inda ya jaddada cewa ya kamata majalisa ta riƙa tantance duk wasu shawarwari daga ɓangaren zartarwa kafin amincewa da su.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa Saraki ya ce majalisar da ke karɓar dukkan buƙatun gwamnati tare da amincewa da su ba tare da bincike da tantancewa ba, ba ta cika nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora mata ba.
