Jam’iyyar PRP ta bayyana rashin amincewarta da yunkurin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na kafa ’yan sandan jihohi ta hanyar yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin Nijeriya, tana mai cewa gwamnatin ba ta da amana da za ta gudanar da irin wannan muhimmin sauyi.
PRP ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Shugabanta na kasa, Alhaji Hakeem Baba-Ahmed, ya fitar, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.
Jam’iyyar ta amince cewa akwai bukatar sake fasalin hukumomin tsaro da na tabbatar da doka domin magance matsalolin rashin tsaro da kuma dawo da amincewar jama’a ga gwamnati da hukumomin kasa.
Sai dai PRP ta ce gwamnatin APC karkashin jagorancin Shugaba Tinubu ta gaza wajen tafiyar da harkokin tsaro, saboda haka ba ta da cikakkiyar kima ko amincewar ’yan Nijeriya da za ta jagoranci sauya tsarin aikin ’yan sanda.
Sanarwar ta ce, duk da cewa gwamnatin na iya samun rinjayen da ake bukata domin yin gyaran kundin tsarin mulki, hakan bai sauya ra’ayinta cewa yunkurin kafa ’yan sandan jihohi a wannan lokaci abin zargi ne kuma bai kamata a amince da shi ba.
Jam’iyyar ta kuma bukaci gwamnatin tarayya ta fi mayar da hankali wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma tare da kawo karshen matsalar rashin tsaro da ke addabar sassan kasar nan.
PRP ta kara da cewa babban zaben shekarar 2027 ya kamata ya zama dama ga ’yan Nijeriya su tantance gwamnati kafin a dauki manyan matakai irin na sauya tsarin aikin ’yan sanda.
A ranar Talata ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa da kudirin gyaran kundin tsarin mulkin da aka yi wa kwaskwarima 1999 domin samar da kafa ’yan sandan jihohi a fadin kasar nan, inda Majalisar Dattawa ta amince da kudirin a ranar Laraba.
