Fitaccen lauya mai rajin kare haƙƙin bil’adama, Femi Falana SAN, ya bayyana cewa kafa ‘yan sandan jihohi ba zai kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro a Nijeriya ba, muddin gwamnati ba ta magance matsalolin talauci da rashin aikin yi ba.
Falana ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels, inda ya ce gwamnati ta fi mayar da hankali kan sauya tsarin tsaro, maimakon magance matsalolin da ke jefa matasa cikin aikata laifuka.
A cewarsa, ana yawan tattaunawa kan yadda za a ƙara yawan ‘yan sanda ko guraren ‘yan sanda, amma ba a ba da muhimmanci ga samar da ayyukan yi, tallafa wa matasa da kuma rage talauci ba.
Falana ya ce idan ba a magance waɗannan matsaloli gaba ɗaya ba, kafa ‘yan sandan jihohi ko ma na ƙananan hukumomi ba zai warware matsalar rashin tsaro da ƙasar ke fuskanta ba.
Ya kuma tunatar da cewa Nijeriya ta taɓa amfani da tsarin ‘yan sanda na yankuna a lokacin Jamhuriya ta Farko, amma daga baya aka soke tsarin saboda yadda wasu shugabannin yankuna suka riƙa amfani da ‘yan sandan wajen cin zarafin abokan hamayyarsu.
Lauyan ya ce idan ana son dawo da tsarin ‘yan sandan jihohi, dole ne a fara tabbatar da an magance matsalolin da suka sa aka soke tsohon tsarin, yana mai cewa kudirin dokar da Majalisar Dokoki ta amince da shi bai fayyace isassun matakan kariya daga yiwuwar amfani da ‘yan sandan jihohi ba.
Haka kuma, Falana ya nuna damuwa kan yadda wasu gwamnatocin jihohi ke fama da matsalar biyan albashi da fansho, yana mai tambayar yadda za su iya ɗaukar nauyin rundunar ‘yan sandan jihohi idan aka kafa ta.
A ranar Laraba ne Majalisar Dattawa ta amince da kudirin gyaran kundin tsarin mulkin 1999 da zai bai wa jihohi damar kafa rundunonin ‘yan sandansu, bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya miƙa kudirin ga majalisar.
