Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da ɗaukar jami’an tsaron gandun daji 1,000 aiki a jihar Katsina, a wani mataki da ake ganin zai ƙara ƙarfafa yaƙi da matsalolin tsaro, musamman hare-haren ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane a jihar.
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ne ya bayyana hakan bayan wata ganawa da malaman addini da sauran masu ruwa da tsaki da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Katsina, inda aka tattauna hanyoyin da al’umma za su taka rawa wajen magance matsalar tsaro.
Gwamna Radda ya bayyana amincewar shugaban ƙasar a matsayin wani babban ci gaba ga ƙoƙarin da gwamnati ke yi na kwato dazuzzuka da yankunan karkara daga hannun ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka.
A cewarsa, sabbin jami’an tsaron gandun dajin za su yi aiki tare da jami’an tsaro na gwamnati da kuma kungiyoyin sa-kai domin ƙara tsaurara matakan tsaro a yankunan da suka daɗe suna zama mafakar masu laifi.
Ya ce za a bai wa jami’an horo na musamman tare da samar musu da kayan aiki domin su iya gudanar da sintiri da sa ido a dazuzzuka da ƙauyukan da ke nesa da birane, waɗanda galibi masu laifi ke amfani da su wajen ɓoye kansu.
Gwamnan ya ƙara da cewa taron da aka yi da malaman addini wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnati na haɗa kan al’umma wajen yaƙi da matsalar ‘yan bindiga da garkuwa da mutane.
A cewarsa, jami’an tsaro kaɗai ba za su iya kawo ƙarshen matsalar ba sai idan al’umma sun bayar da haɗin kai ta hanyar samar da sahihan bayanan sirri da kuma goyon bayan matakan da gwamnati ke ɗauka.
Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da ƙoƙarin samar da sababbin hanyoyin magance matsalolin tsaro a jihohin Arewa maso Yamma da suka fi fama da hare-haren ‘yan bindiga a cikin shekaru da suka gabata.
