Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta yi watsi da rahotannin da ke cewa tana shirin ƙaƙaba sabbin haraji kan harkokin sadarwa da man fetur, tana mai bayyana cewa irin waɗannan rahotanni ba su da tushe kuma ba su da makama.
Ma’aikatar kuɗi ta Nijeriya ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da shugaban sashen yaɗa labarai na ma’aikatar, Efe Ovuakporie, ya fitar a ranar Laraba.
Sanarwar ta zo ne bayan wasu rahotanni sun danganta gwamnatin da shawarwarin da asusun lamuni na duniya, ya bayar a sabon rahotonsa kan tattalin arzikin Nijeriya.
Rahotannin sun yi ikirarin cewa IMF ya ba da shawarar a fara karɓar harajin VAT kan man fetur tare da ƙaƙaba harajin musamman kan kamfanonin sadarwa domin ƙara kuɗaɗen shiga da tallafa wa ayyukan ci gaba.
Sai dai gwamnatin ta bayyana cewa rahoton IMF ya ƙunshi shawarwari ne kawai da asusun ya gabatar domin gwamnati ta yi nazari a kansu, kuma ba umarni ba ne ko wata manufa da Nijeriya ta amince da aiwatarwa.
Sanarwar ta jaddada cewa duk wani mataki da ya shafi haraji a Nijeriya yana bin hanyoyin doka da kundin tsarin mulki, tare da la’akari da muradun ƙasa da halin tattalin arziki da jama’a ke ciki.
Gwamnatin ta kuma tabbatar da cewa har yanzu ragin VAT da aka yi wa fetur yana nan daram, kuma ba a soke shi ba.
Haka kuma ta ce babu wani shiri a halin yanzu na fara aiwatar da ƙarin kuɗin haraji ko caji kan man fetur.
A cewar gwamnatin, ci gaba da dakatar da irin waɗannan haraji ya taimaka wajen rage tasirin tashin farashin makamashi a duniya kan rayuwar jama’a da harkokin kasuwanci, tare da taimakawa wajen daidaita farashin man fetur a cikin gida.
Saboda haka, gwamnatin ta bukaci al’umma da su yi watsi da rahotannin da ke cewa ana shirin ƙaƙaba sabbin haraji kan kamfanonin sadarwa ko man fetur, tana mai cewa babu wani tsari makamancin haka a gaban gwamnati.
Ta ƙara da cewa a halin yanzu hankalinta ya karkata ne wajen bunƙasa tattalin arziki, inganta hanyoyin tattara kuɗaɗen shiga, rage almundahana da kuma samar da yanayi mai kyau ga masu zuba jari da samar da ayyukan yi.
A ƙarshe, gwamnatin ta tabbatar wa ‘yan ƙasa cewa duk wani sabon matakin haraji da za a ɗauka nan gaba za a sanar da shi a hukumance ta hanyoyin gwamnati tare da bin duk matakan doka da suka dace.
