‘Yan wasa 10 da suka lashe kyaututtukan Ballon d’Or za su fafata a wasan kusa da na ƙarshe na Gasar Kofin Duniya ta 2026.
Za a ga fitattun ‘yan wasa 10 da suka taɓa lashe kyaututtukan Ballon d’Or da sauran manyan lambobin yabo a wasan kusa da na ƙarshe na Gasar Kofin Duniya ta FIFA ta 2026, inda ƙasashen Faransa, Sifaniya, Argentina da Ingila za su fafata domin neman gurbin zuwa wasan ƙarshe.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Sifaniya za ta kara da Faransa a ranar Talata, yayin da Argentina za ta fafata da Ingila a ranar Laraba domin samun tikitin zuwa wasan ƙarshe na gasar.
Tsoffin gwarazan Ballon d’Or uku ne har yanzu ke fafatawa domin lashe Kofin Duniya.
Sun haɗa da kyaftin ɗin Argentina Lionel Messi, wanda ya lashe kyautar har sau takwas, ɗan wasan tsakiya na Sifaniya Rodri, da kuma ɗan wasan gaba na Faransa Ousmane Dembélé.
Mai tsaron ragar Argentina Emiliano Martínez shi ne kaɗai cikin waɗanda suka lashe kyautar Yashin Trophy sau biyu da har yanzu suke cikin gasar.
Haka kuma, ‘yan wasa huɗu da suka lashe Copa Trophy, wadda ake bai wa mafi kyawun ɗan wasa ɗan ƙasa da shekara 21, suna cikin waɗanda za su fafata.
Sun haɗa da Lamine Yamal, Pedri da Gavi na Sifaniya, da Jude Bellingham na Ingila.
Kazalika, kyaftin ɗin Faransa Kylian Mbappé da ɗan wasan gaba na Ingila Harry Kane, waɗanda suka raba Gerd Müller Trophy ta shekarar 2024 a matsayin fitattun masu zura ƙwallaye, su ma suna cikin jerin ‘yan wasan da za su fafata a wasannin da za a buga.
