DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeKetareIran ta fara shirye-shiryen gudanar da jana'izar Ayatollah Ali Khamenei

Iran ta fara shirye-shiryen gudanar da jana’izar Ayatollah Ali Khamenei

Iran ta fara shirye-shiryen gudanar da jana’izar tsohon Jagoran Addini na ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei, bayan da aka halakashi a hare-haren sama da Amurka da Isra’ila suka kai yayin rikicin da ya ɓarke a Gabas ta Tsakiya.

Kamfanin dillancin labarai na AFP, ya ce an kafe manyan hotunan marigayin a harabar Grand Mosalla da ke birnin Tehran, yayin da ma’aikata ke ci gaba da shirya wurin domin jana’izar da za a gudanar.

Rahotonni sun bayyana cewa an jinkirta jana’izar ne saboda tsananin rikicin da ya gudana tsakanin Iran da Amurka, amma yanzu ana shirin gudanar da ita bayan da ɓangarorin biyu suka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta wucin gadi.

Ayatollah Ali Khamenei, wanda ya rasu yana da shekaru 86, an halaka shi ne a ranar 28 ga Fabrairu, ranar farko ta yaƙin, a gidansa da ke tsakiyar birnin Tehran.

A ranar Asabar ne za a fara jana’izar jama’a, inda za a ajiye gawarsa a Grand Mosalla, wani katafaren wuri da ake gudanar da sallar Juma’a, manyan tarukan gwamnati da kuma bukukuwan addini.

Haka kuma, za a gabatar da gawarwakin wasu ‘yan uwansa da aka halaka tare da shi domin jama’a su yi musu bankwana.

Mahukuntan Iran sun bayyana cewa ana sa ran tsakanin mutane miliyan 15 zuwa 20 za su halarci jana’izar, abin da zai sa ta zama mafi girman jana’izar da aka taɓa yi a tarihin ƙasar.

A yayin shirye-shiryen, an sake fentin wuraren taron, an tsaurara matakan tsaro, yayin da kafafen yaɗa labaran gwamnati ke nuna yadda ake kammala gine-gine a harabar wurin.

Saboda taron jama’a da ake sa ran zai yi yawa, gwamnatin Iran ta bukaci mahalarta su yi amfani da motocin sufuri na gwamnati maimakon motocinsu tare da ba su shawarar shan ruwa sosai saboda tsananin zafi da ake sa ran za a fuskanta.

A ranar Juma’a kuma, za a gudanar da wani taro na musamman domin shugabannin ƙasashe da wakilan gwamnatoci, inda ake sa ran wakilai daga kusan ƙasashe 30 za su halarta, ciki har da Iraki, Afghanistan da Pakistan.

Gwamnatin Iran ta ayyana ranakun jana’izar a matsayin hutun aiki a birnin Tehran da kuma biranen Qom da Mashhad, tare da sanya takunkumin zirga-zirga a yawancin sassan babban birnin.

Bayan kammala jana’izar a Tehran, za a kai gawar Ayatollah Khamenei zuwa biranen Najaf da Karbala na ƙasar Iraki, kafin daga bisani a binne shi ranar 9 ga Yuli a harabar Imam Reza Shrine da ke birnin Mashhad, inda aka haife shi.

Har zuwa yanzu, ba a tabbatar ko sabon Jagoran Addini kuma ɗansa, Mojtaba Khamenei, zai halarci jana’izar ba, domin jami’an da ke kula da shirye-shiryen sun ce ba su da bayanin hakan a wannan lokaci.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata