Dan takarar shugabancin Nijeriya na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya bukaci hukumar zaɓe INEC da ta wallafa takardun shaidar karatu da sauran takardun da ke nuna cancanta da dukkan ’yan takarar da ke neman kujeru daban daban da suka gabatar domin tabbatar da gaskiya da ƙarfafa amincewar jama’a da tsarin zaɓe.
Obi ya bayyana hakan ne yayin da yake tsokaci kan tambayoyin da ke cikin fom ɗin tsayar da takara na INEC, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Ya ce bayyana takardun a bainar jama’a zai taimaka wajen tabbatar da cewa masu neman shugabanci suna da gaskiya da rikon amana.
Ya ce ɗaya daga cikin tambayoyin da ke cikin fom ɗin na neman sanin ko ɗan takara ya taɓa gabatar wa INEC takardar shaidar karatu ta bogi?
Obi ya ce idan har ana buƙatar amsa irin wannan tambaya, babu dalilin da zai hana INEC ta wallafa takardun shaidar karatu da sauran bayanan cancantar dukkan ’yan takara domin jama’a su gani da idonsu.
A cewarsa, yin hakan zai ƙarfafa dimokuraɗiyya tare da ƙara wa jama’a kwarin gwiwa kan gaskiya da adalcin tsarin zaɓe.
Ya kuma yi nuni da wata tambaya da ke cikin sashe na E na fom ɗin, wadda ke tambayar ko an taɓa ayyana ɗan takara a matsayin wanda ba shi da cikakken hankali, yana mai cewa halin da Nijeriya ke ciki ya sa ya dace a tambayi ko shugabanni na da cikakken hangen nesa wajen tafiyar da mulki.
Obi ya ce matsalolin da suka haɗa da yawaitar satar mutane, rashin tsaro a manyan hanyoyi, yunwa da kuma zargin karkatar da kuɗaɗen gwamnati sun nuna cewa akwai buƙatar shugabanci mai ɗaukar matakan gaggawa domin ceto ƙasar.
Ya bayyana cewa shugabanci nagari zai dubi matsalolin tsaro da tattalin arziki a matsayin dokar ta-ɓaci, tare da haɗa hukumomin tsaro, masana da shugabannin al’umma domin nemo mafita cikin gaggawa.
A cewarsa, rayuwar ‘yan Nijeriya, tsaronsu da kuma zaman lafiyar ƙasa ya kamata su kasance a gaba fiye da siyasa ko anfani na jam’iyyu, yana mai cewa ƙasar na buƙatar shugabanni masu ƙwarewa, nagarta, tausayi da jajircewa wajen yi wa jama’a hidima.
Tun da farko, Jagoran Jam’iyyar NDC na Ƙasa, Sanata Seriake Dickson, ya tabbatar da cewa an riga an ɗora sunan Peter Obi a shafin INEC domin tsayawa takara, duk kuwa da hukuncin kotu da ya soke tsarin rajistar jam’iyyar.
