Kungiyar Masu Gidajen Mai Masu Zaman Kansu ta Nijeriya (IPMAN) ta yi barazanar cewa za ta rufe gidajen mai a faɗin ƙasar nan idan har Gwamnatin Tarayya ta yi yunƙurin kayyade farashin fetur a kasuwa.
Mai magana da yawun ƙungiyar, Chinedu Ukadike, ne ya bayyana hakan a wata hira, yana mai cewa ba za a iya tilasta wa masu kasuwanci sayar da fetur a farashin da gwamnati ta ƙayyade ba a kasuwar da aka soke tsarin kayyade farashi.
Barazanar ta biyo bayan kalaman Minista karƙashin Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur, Heineken Lokpobiri, wanda ya ce gwamnati ba za ta lamunci cin zarafin masu amfani da fetur ta hanyar tsadar farashi ko riba mai yawa ba.
Ministan ya bayyana haka ne a wajen taron masu ba da shawara kan harkokin shari’a na Hukumar NMDPRA a Abuja, inda ya ce duk da cewa an soke tsarin kayyade farashin fetur, hakan ba yana nufin hukumomi za su yi watsi da kare haƙƙin masu amfani ba.
Kalaman nasa sun zo ne yayin da ake ci gaba da nuna damuwa kan yadda farashin fetur bai sauka sosai ba duk da raguwar farashin danyen mai a kasuwar duniya daga kusan dala 120 zuwa kusan dala 72 kan ganga.
jaridar Punch ta ruwaito Ukadike ya musanta zargin cewa masu gidajen mai na cin riba fiye da kima, yana mai cewa da dama daga cikinsu na tafka asara sakamakon sauye-sauyen farashi da matatar Dangote ke yi.
Ya ce, “Idan gwamnati ta yi ƙoƙarin kayyade farashi, za mu rufe gidajen mai a faɗin ƙasar nan. Ba za ka iya kayyade farashi a kasuwar da aka soke tsarin kayyade farashi ba. Dole ne a fara sanin farashin da muka sayi fetur kafin a ce mu sayar da shi a wani farashi.”
Ukadike ya ƙara da cewa masu gidajen mai da dama sun sayi fetur da tsada, amma kafin su kai shi gidajensu sai farashi ya ragu, lamarin da ya jefa su cikin asara. Ya ce baya ga haka, yawancinsu na gudanar da kasuwancinsu ne da rancen banki, wanda ba ya sauyawa duk lokacin da farashin fetur ya sauya.
A cewarsa, abin da gwamnati ya kamata ta fi mayar da hankali a kai shi ne ƙarfafa gasa ta hanyar tabbatar da matatun mai na cikin gida sun fara aiki yadda ya kamata, tare da buɗe damar shigo da fetur daga ƙasashen waje.
Ya ce idan aka samu cikakkiyar gasa tsakanin masu tace mai da masu shigo da shi, farashin fetur zai ragu ta hanyar ƙarfin kasuwa ba tare da buƙatar gwamnati ta kakaba farashi ba.
A nasa ɓangaren, Shugaban Ƙungiyar Masu Gidajen Mai ta PETROAN, Billy Gillis-Harry, ya ce gwamnati na da ikon sa baki domin kare masu amfani da fetur, amma ya kamata ta fara tattaunawa da dukkan masu ruwa da tsaki kafin ɗaukar duk wani mataki.
Ya buƙaci Ministan Man Fetur da ya kira taron masu ruwa da tsaki domin a tattauna matsalolin da ke haddasa tsadar fetur tare da cimma matsayar da za ta amfani ’yan Nijeriya.
A halin yanzu dai, farashin litar fetur na ci gaba da kai tsakanin naira 1,140 zuwa 1,210 a sassa daban-daban na ƙasar.
