Jam’iyyar NDC ta ware tikitin takarar shugaban ƙasa na shekarar 2027 ga yankin kudancin Nijeriya, matakin da ake ganin zai ƙara wa tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, damar tsayawa takara.
An sanar da wannan mataki ne a ranar Asabar yayin babban taron jam’iyyar na ƙasa da ke gudana a Abuja.
Jam’iyyar ta kuma tabbatar da hakan a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Manyan jiga-jigan jam’iyyar ne ke halartar taron, ciki har da Obi da kuma tsohon Gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.
Bisa ga tsarin ajandar taron da aka bai wa manema labarai, batutuwan da za a tattauna sun haɗa da rabon mukamai (zoning), amincewa da kundin tsarin mulkin jam’iyyar da aka gyara, da kuma zaɓen shugabannin jam’iyyar na ƙasa.
A kwanakin baya, jam’iyyar ta samu karuwar shigowar ‘yan siyasa daga wasu jam’iyyun, ciki har da ADC da PDP
A ranar Talata, ‘yan majalisar wakilai 17 sun sauya sheka daga ADC zuwa NDC yayin zaman majalisa.
Wannan sauyin ya biyo bayan shigar Obi da Kwankwaso cikin NDC ne kwanaki biyu bayan sun fice daga ADC.
