Wasu dalibai da suka ci gajiyar shirin asusun lamunin karatu na Nijeriya NeLFund a Jihar Anambra sun bayyana goyon bayansu ga shugaba Bola Tinubu domin sake tsayawa takara karo na biyu, tare da bayar da gudummawar Naira miliyan 10.7 domin sayen fom ɗin nuna sha’awa.
Daliban sun ce sun yi haka ne domin nuna jin daɗinsu kan yadda shirin lamunin ya taimaka wajen sauƙaƙa samun ilimi mai zurfi da kuma rage nauyin kuɗaɗen karatu a kansu, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Da yake jawabi yayin gabatar da gudummawar a Jami’ar Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu a ranar Juma’a, shugaban ƙungiyar daliban Nijeriya (NANS), reshen Jihar Anambra, Ifeanyichukwu Chukwuemeka, ya bayyana cewa wannan mataki alama ce ta godiya ga sauye-sauyen da Tinubu ya kawo a fannin ilimi da kuma manufofinsa da suka mayar da hankali kan matasa.
Haka kuma daliban sun yaba wa ɗan kasuwa Obinna Iyiegbu (Obi Cubana), wanda shi ne mai kula da yankin Kudu maso Gabas na ƙungiyar City Boys Movement, bisa goyon bayan da yake bai wa ci gaban matasa.
Sun kuma yaba wa shugabar mata ta jiha a ƙungiyar, Adaora Soludo, da kuma mai kula da harkokin ƙungiyar a jihar, Nonso Ozoemena, kan gudummawar da suke bayarwa wajen tara matasa da bunƙasa shugabanci a Jihar Anambra.
