DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, July 8, 2026
HomeLabaraiJapan ta kara kudin biza da kashi 400 ga ‘yan Nijeriya da...

Japan ta kara kudin biza da kashi 400 ga ‘yan Nijeriya da wasu kasashen

Gwamnatin Japan ta amince da karin kudin biza ga ‘yan Nijeriya da sauran wasu kasashe bayan yin kwaskwarima ga dokar da ke kula da harkokin biza a kasar.

Rahotanni sun nuna cewa an amince da matakin ne a wani taron majalisar ministocin kasar da aka gudanar ranar Juma’a, wanda ya zama karo na farko da aka sake duba kudin biza cikin shekaru 48 tun daga shekarar 1978.

Sabon tsarin ya tanadi karin kudin bizar shiga sau daya daga yen 3,000 zuwa yen 15,000, yayin da kudin bizar shiga sau da dama zai tashi daga yen 6,000 zuwa yen 30,000.

Za a fara amfani da sabbin kudaden ne ga duk masu neman biza daga ranar 1 ga watan Yuli.

Ministan Harkokin Wajen Japan, Toshimitsu Motegi, ya ce an dauki matakin ne domin daidaita kudaden da hauhawar farashi da kuma sauye-sauyen darajar kudade suka haifar tsawon shekaru.

Ya kuma bayyana cewa gwamnati ba ta sa ran karin kudin zai yi tasiri kai tsaye ga yawan masu ziyartar kasar daga kasashen waje.

A watan da ya gabata, majalisar dattawan Japan ta amince da wata doka da ke bai wa gwamnati damar kara wasu kudaden da suka shafi biza da takardun zama har sau 30 na abin da ake biya a yanzu.

Sabuwar dokar ta kuma kara iyakar kudin da ake iya karba wajen sauya matsayin zama ko tsawaita izinin zama daga yen 10,000 zuwa yen 100,000.

Haka zalika, iyakar kudin neman zama na dindindin ta tashi daga yen 10,000 zuwa yen 300,000.

Gwamnatin Japan ta ce karin kudaden zai taimaka wajen biyan bukatun kula da yawan bakin da ke karuwa a kasar, wanda ya kai mutum miliyan 4.13 zuwa karshen shekarar 2025.

Jami’ai sun kuma ce za a yi amfani da kudaden wajen fadada shirye-shiryen koyar da harshen Japan da kuma karfafa matakan dakile zaman baki ba bisa ka’ida ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata