Dan majalisar dokokin jihar Bauchi mai wakiltar mazabar Sakwa, Hon. Wanzam Mohammed Zaki, ya rasu a safiyar Lahadi a birnin Bauchi bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.
Marigayin har ya zuwa lokacin rasuwarsa shi ne Shugaban Kwamitin Majalisar kan Kasafi da Ƙididdiga.
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, Rt. Hon. Abubakar Y. Sulaiman, ne ya sanar da rasuwar cikin wata sanarwa da kakakinsa, Mukhtar Garba Kobi, ya sanya wa hannu. Ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai jajircewa da sadaukarwa wajen hidimar al’umma da ci gaban jihar.
A cikin sanarwar, shugaban majalisar ya ce rasuwar Hon. Wanzam ta bar babban gibi a majalisar dokoki da ma al’ummar mazaɓarsa ta Sakwa. Ya ce marigayin ya taka rawar gani wajen gudanar da ayyukan majalisa musamman a fannin kasafi da kula da kuɗaɗen gwamnati.
An bayyana cewa kafin rasuwarsa, marigayin ya kasance ɗaya daga cikin fitattun ‘yan majalisa masu kishin ci gaba, tare da bayar da gudummawa wajen tsara manufofi da ayyukan da ke shafar rayuwar al’umma.
An gudanar da sallar jana’izar marigayin a Masallacin Juma’a na Gwallaga da ke birnin Bauchi a ranar Lahadi da ƙarfe 11:00 na safe, inda jama’a da dama suka halarta domin yi masa addu’a ta ƙarshe.
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa kan rasuwar, yana mai cewa jihar ta yi babban rashi na ɗan majalisa mai gaskiya, ladabi da kishin jama’a.
A cikin saƙon da mai ba shi shawara kan yaɗa labarai, Mukhtar Gidado, ya fitar, gwamnan ya bayyana marigayin a matsayin jagora mai tawali’u da jajircewa wajen hidimar jama’a da ci gaban jihar.
Gwamna Bala Mohammed ya ƙara da cewa gudummawar marigayin a majalisa, musamman a kwamitin kasafi da ƙididdiga, ta taimaka wajen inganta manufofi da ayyukan gwamnati da suka shafi rayuwar jama’a.
Ya ce rasuwar Hon. Wanzam babban rashi ne ba ga iyalansa kaɗai ba, har ma ga al’ummar jihar Bauchi baki ɗaya, inda ya yi addu’ar Allah ya jikansa da rahama.
Gwamnan ya kuma roƙi jama’a da su riƙa ɗaukar darasi daga rayuwar marigayin ta fuskar sadaukarwa da hidimar jama’a, tare da addu’ar Allah ya ba shi Aljannatul Firdaus.
