Wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP da Kabiru Tanimu Turaki ke jagoranta sun kai ziyara ga tsohon shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan a Abuja.
Ziyarar ta zo ne ƙasa da awanni 24 bayan rahotanni sun ce Jonathan ya shaida wa magoya bayansa cewa zai yi shawarwari kan kiraye-kirayen da ake yi masa na ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ganawar na daga cikin jerin shawarwari da ake yi kan makomar jam’iyyar.
Turaki ya je tare da mambobin kwamitinsa na aiki da kuma wasu shugabannin jam’iyyar.
Da yake magana kan ziyarar, kakakin kwamitin, Ini Ememobong, ya bayyana cewa suna na ci gaba da ganawa da manyan masu ruwa da tsaki a faɗin ƙasar.
Ya kuma bayyana cewa a baya sun gana da tsohon shugaban mulkin soja Ibrahim Babangida, tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, da kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasa Namadi Sambo.
A wani ɓangare kuma, tsohon shugaban ƙasar Goodluck Jonathan a ranar Juma’a ya kalubalanci ƙarar da wani lauya, Johnmary Jideobi, ya shigar domin hana shi tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
