DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, October 5, 2026
HomeLabaraiNijeriya ta biya harajin $22.5m kan bashin $1.5bn daga bankin UAE -...

Nijeriya ta biya harajin $22.5m kan bashin $1.5bn daga bankin UAE – DMO

Gwamnatin Nijeriya ta biya dala miliyan 22.5 a matsayin haraji kan bashin dala biliyan 1.5 da ta karɓa daga First Abu Dhabi Bank (FAB) a zango na biyu na 2026.

Bayanan Ofishin Kula da Basussukan Nijeriya (DMO) sun nuna cewa kuɗin ya kai kashi 1.5 cikin 100 na dala biliyan 1.5 da aka karɓa daga cikin shirin rancen dala biliyan 5 da aka amince da shi.

Bayanan biyan bashin ƙasashen waje daga Afrilu zuwa Yuni sun nuna cewa an sanya dala miliyan 22.5 ɗin ƙarƙashin “other charges”, ba tare da an nuna biyan babban bashin ko ruwa ba.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, DMO ba ta bayyana irin kuɗin da aka biya ba, abin da ya bar tambaya kan ko kuɗin ya shafi tsara yarjejeniyar, ciniki ko wasu kuɗaɗe ne.

Nijeriya ta samu amincewar shirin Total Return Swap na dala biliyan 5 daga FAB domin samun kuɗin waje da kuma tallafa wa kasafin kuɗin 2026. Gwamnati ta karɓi dala biliyan 1.5 daga cikin shirin a watan Yuni.

A ƙarƙashin yarjejeniyar, gwamnati na karɓar kuɗin dala yayin da take bayar da takardun bashin gwamnati na naira a matsayin jingina.

DMO ta ce ana iya bayar da jinginar da ta kai kashi 133.3 cikin 100 na adadin kuɗin da aka karɓa. Hakan na iya nufin jinginar takardun gwamnati da darajarsu ta kai kusan dala biliyan biyu kan bashin dala biliyan 1.5.

Jimillar “other charges” da Nijeriya ta biya kan basussukan ƙasashen waje a wannan zango ta kai dala miliyan 39.25. Kudin FAB na dala miliyan 22.5 ya kai kusan kashi 57.3 cikin 100 na wannan adadi.

Baya ga wannan, Nijeriya ta biya FAB dala miliyan 33.38 a matsayin ruwa kan rance na hadin guiwar bankuna a wannan zango. Ya zuwa ƙarshen Yuni, bashin Nijeriya ga bankin ya kai kusan dala biliyan 3.37.

Yarjejeniyar ta fuskanci gargadi daga IMF, wanda ya ce irin wannan tsarin na iya kasancewa ba a bayyane yake sosai kuma yana iya haifar da ƙarin haɗarin kuɗi. Fitch Ratings ma ta yi gargadin yiwuwar ƙarin haɗarin kula da bashi da kuɗin gwamnati.

Sai dai DMO ta kare yarjejeniyar, tana mai cewa tsarin na samar da wata hanya ta samun kuɗin waje tare da tanadin matakan kariya daga haɗarin canjin kuɗi, kuɗin ruwa, darajar jingina da sake neman kuɗin biyan bashin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata