DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeLabaraiJonathan, Obi da Makinde sun samu tikitin takarar shugaban ƙasa na 2027

Jonathan, Obi da Makinde sun samu tikitin takarar shugaban ƙasa na 2027

Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, da tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, da gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, sun samu tikitin takarar shugaban ƙasa a jam’iyyunsu daban-daban domin zaɓen 2027.

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, Jonathan ya samu amincewar wani ɓangare na jam’iyyar PDP a wani taro na musamman da aka gudanar a Abuja, yayin da Peter Obi ya karɓi tikitin jam’iyyar Nigerian Democratic Coalition (NDC), sannan Seyi Makinde ya zama ɗan takarar jam’iyyar Allied People’s Movement (APM).

Taron ɓangaren PDP ya fuskanci tangarda bayan jami’an tsaro sun rufe wurin taron, yayin da wasu da ake zargin ‘yan daba ne suka kai hari kan mahalarta taron. Duk da haka, shugabannin ɓangaren sun tabbatar da amincewa da Jonathan a matsayin ɗan takararsu tare da ba shi takardar shaidar cin zaɓe ta wakilci.

A jawabinsa, Peter Obi ya yi alƙawarin magance matsalolin tsaro da tattalin arziki da wutar lantarki tare da faɗaɗa tsarin inshorar lafiya idan aka zaɓe shi.

Shi ma Makinde ya gabatar da abin da ya kira “Reset Nigeria Agenda”, inda ya yi alƙawarin sake fasalin harkokin mai, tsaro da noma domin inganta rayuwar ‘yan Nijeriya.

Lamarin na zuwa ne yayin da jam’iyyun siyasa ke ƙara ɗaukar matakai gabanin babban zaɓen 2027, inda ake sa ran fafatawar siyasa za ta ƙara zafi a watanni masu zuwa.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata