DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, July 8, 2026
HomeLabaraiDavido: Abokantaka da Seyi Tinubu ba za ta hana ni faɗin gaskiya...

Davido: Abokantaka da Seyi Tinubu ba za ta hana ni faɗin gaskiya ba

Fitaccen mawakin Afrobeats, Davido, ya bayyana cewa abokantakarsa da Seyi Tinubu ba ta hana shi bayyana damuwarsa kan matsalolin rashin tsaro da rashin adalci da ke addabar Nijeriya.

Mawakin, wanda sunansa na asali David Adeleke, ya bayyana hakan ne bayan ce-ce-ku-cen da suka biyo bayan wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X inda ya ce masu nishaɗi, har da shi kansa, ba sa yin magana sosai kan matsalolin da ke damun ‘yan Nijeriya.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa wasu masu amfani da shafukan sada zumunta sun zargi Davido da nuna halin munafunci saboda kusancinsa da iyalan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, musamman Seyi Tinubu.

Sai dai Davido ya musanta kasancewa cikin wata ƙungiyar siyasa ta “City Boys”, yana mai cewa abokantakarsa da Seyi Tinubu ta tsaya ne a matsayin abokai kawai. Ya ƙara da cewa sau da yawa yana isar masa da koke-kokensa kan halin da ƙasa ke ciki kai tsaye.

Mawakin ya kuma tunatar da cewa a baya ya sha suka bayan ya yi magana kan matsalolin Nijeriya a wasu kafafen yaɗa labarai na ƙasashen waje, yana mai jaddada cewa zai ci gaba da bayyana ra’ayinsa kan batutuwan da suka shafi al’umma.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata