Shugaban jam’iyyar PRP a Nijeriya, Dr Hakeem Baba-Ahmed, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu, zai iya shan kaye tun kafin ƙarfe 4 na yamma a ranar zaɓen shugaban ƙasa na 2027, idan aka gudanar da zaɓen cikin ’yanci, adalci da sahihanci.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Baba-Ahmed ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels, inda ya ce sakamakon zaɓen gwamnan Osun na baya-bayan nan ya nuna cewa jam’iyyar APC za ta iya fuskantar ƙalubale idan aka bar ƙuri’un jama’a su tantance wanda zai yi nasara.
Ya ce nasarar da Gwamna Ademola Adeleke ya samu a Osun, duk da ƙarfin da APC ke da shi a matakin tarayya da jihohi da kuma majalisar dokoki na nuna cewa jam’iyyar da ke mulki ba ta da tabbacin samun nasara idan aka gudanar da zaɓe cikin gaskiya.
Baba-Ahmed ya ce abin da ya faru a Osun ya bambanta da wasu zaɓuka, domin a cewarsa, babu wata babbar ƙawancen jam’iyyun adawa da ta haɗa kai domin kayar da APC, amma duk da haka jam’iyyar ta sha kaye.
Ya ce wannan na iya maimaituwa a matakin ƙasa a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
“Babu wani dalili da zai hana abin da ya faru a Osun maimaituwa a matakin ƙasa,” in ji shi.
Shugaban PRP ɗin ya kuma yi watsi da rade-radin cewa akwai wata yarjejeniya tsakanin Shugaba Tinubu da Gwamna Adeleke da ta taimaka wajen samun sakamakon zaɓen Osun.
A cewarsa, hasashensa ya samo asali ne daga yadda masu zaɓe za su iya kayar da jam’iyyar da ke mulki ta hanyar ƙuri’unsu idan aka ba su damar yin zaɓe cikin ’yanci.
Baba-Ahmed ya kuma soki yadda ake tafiyar da jam’iyyar APC, inda ya bayyana ta da kalamai masu tsauri, yana mai cewa jam’iyyar tana fama da rikice-rikicen cikin gida.
Ya ce duk da cewa Shugaba Tinubu na da goyon bayan gwamnoni da dama da kuma rinjayen mambobin majalisar dokoki ta kasa, hakan ba ya nufin cewa yana da tabbacin lashe zaɓen 2027.
Ya jaddada cewa idan aka gudanar da zaɓen 2027 cikin sahihanci, ’yanci da adalci, yana da yakinin cewa Shugaba Tinubu zai sha kaye.
Da yake bayanin dalilin da ya sa ya ambaci ƙarfe 4 na yamma, Baba-Ahmed ya ce bai son yin hasashen cewa za a san sakamakon tun kafin ƙarfe 12 na rana ba, amma yana ganin cikin ƴan sa’o’i bayan fara kaɗa ƙuri’a za a iya fahimtar inda sakamakon ke dosa.
Ya kuma yi kira ga jama’a da kada su yi gaggawar yabawa INEC kan shirye-shiryen zaɓen 2027, yana mai cewa babban gwajin hukumar zai kasance lokacin da za ta gudanar da zaɓen shugaban ƙasa wanda Shugaba Tinubu yake neman sake komawa.
Baba-Ahmed ya ce sahihancin zaɓen 2027 zai kasance muhimmi wajen tabbatar da amincewar jama’a da tsarin dimokuraɗiyyar Nijeriya, yana mai gargadin cewa rashin gudanar da zaɓen cikin adalci na iya jefa dimokuraɗiyyar ƙasar cikin babban haɗari.
