DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, October 6, 2026
HomeSiyasaKo ina barci ko ina cin abinci, tunanina shi ne Tinubu ya...

Ko ina barci ko ina cin abinci, tunanina shi ne Tinubu ya sake cin zaɓe — Wike

Ministan birnin tarayyar Nijeriya Abuja, Nyesom Wike, ya ce a halin yanzu babban abin da ya fi ɗaukar hankalinsa shi ne ganin shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Wike ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin tarukan ganawa da al’umma da ya gudanar da masarautun Rumueme da Apara a ƙaramar hukumar Obio-Akpor ta jihar Rivers.

Tsohon gwamnan jihar Rivers ya ce tunanin sake zaɓen Tinubu ya mamaye hankalinsa a kullum, yana mai cewa duk abin da yake yi a yanzu yana da alaƙa da ƙoƙarin ganin shugaban ƙasar ya samu goyon baya a zaɓen 2027.

Wike ya bayyana cewa hatta lokacin da yake barci ko cin abinci, batun sake zaɓen Tinubu na cikin abubuwan da yake tunani akai.

Ya kuma yi kira ga mazauna jihar Rivers da su ajiye bambancin ra’ayin siyasa gefe, su kuma goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027.

A cewarsa, gwamnatin Tinubu ta nuna wa al’ummar Rivers cewa tana kula da su ta hanyar naɗe-naɗe da aka bai wa ’yan jihar da kuma wasu ayyukan raya ƙasa da ya ce ana gudanarwa a jihar.

Wike ya ce ya kamata al’ummar Rivers su yaba wa Tinubu kan abubuwan da ya bayyana a matsayin alfanun dimokuraɗiyya da kuma mukaman da aka bai wa wasu ’yan jihar.

Ya kuma yi iƙirarin cewa sake zaɓen Tinubu a 2027 zai kasance mai sauƙi fiye da zaɓen 2023, yana mai kira ga magoya bayansa da su yi ƙoƙarin ganin shugaban ƙasar ya samu kuri’u masu yawa.

Ministan ya kuma yi magana kan wasu ’yan siyasar adawa da ake sa ran za su fafata a zaɓen 2027, ciki har da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da tsohon gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi, waɗanda ke da alaƙa da Jam’iyyar ADC.

Wike ya nuna shakku kan ƙarfin tikitin ADC a jihar Rivers, yana mai cewa jam’iyyar za ta iya fuskantar ƙalubale wajen samun kashi 25 cikin 100 na ƙuri’un jihar da kundin tsarin mulki ya tanada domin ɗan takarar shugaban ƙasa.

Haka kuma, ya yi kalamai kan tsohon Gwamnan Anambra kuma ɗan takarar shugaban ƙasa Peter Obi da sauran ’yan siyasar adawa, inda ya bayyana ra’ayinsa cewa ba su da damar samun nasara a zaɓen.

Wike ya kuma yi kira ga magoya bayansa da abokan siyasarsa a Rivers da su guji rikice-rikicen cikin gida da kuma sabani tsakanin al’ummomi, yana mai cewa irin waɗannan matsaloli na iya kawo cikas ga harkokin siyasarsu yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.

Ya ce ’yan siyasa ba sa bukatar kashe kansu ko shiga rikici saboda neman kujerar siyasa, yana mai jaddada cewa abin da Allah ya ƙaddara shi ne zai faru.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata