Shugaban wani ɓangare na Jam’iyyar PDP, Kabiru Turaki, ya gargaɗi ’yan Nijeriya da su guji karɓar kuɗi, taliya ko wasu abubuwa daga ’yan siyasa a matsayin musayar ƙuri’unsu a zaɓen 2027.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa Turaki ya yi wannan gargaɗin ne a ranar Litinin a wani taron tunawa da cikar Gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed, shekara 68, wanda aka gudanar a jihar gabanin babban zaɓen 2027.
Turaki ya ce musamman matasa ya kamata su ƙara shiga harkokin siyasa, su fahimci muhimmancin ƙuri’arsu tare da zaɓar shugabannin da suke ganin za su iya wakiltar muradun al’umma.
Ya ce bai kamata matashi ya jira sai an ba shi kuɗi ko wani abu kafin ya yanke shawarar wanda zai zaɓa ba, yana mai cewa hakan na iya rage damar da ɗan ƙasa ke da ita wajen neman shugabanci nagari da riƙon shugabanni da alhaki.
Turaki ya yi kira ga matasan Nijeriya da su daina kallon kansu a matsayin “shugabannin gobe” kawai, yana mai cewa ya kamata su fara taka rawa a harkokin shugabanci da siyasa tun yanzu.
A cewarsa, shekaru na iya wucewa ana ci gaba da gaya wa matasa cewa su ne shugabannin gobe, ba tare da an samar musu da damar taka muhimmiyar rawa a harkokin mulki da yanke shawara ba.
Ya kuma ce al’umma na samun irin shugabancin da ta taimaka wajen samarwa, don haka ’yan ƙasa na da muhimmiyar rawa wajen tabbatar da cewa mutanen da suka cancanta sun samu damar shiga majalisu da sauran mukaman siyasa.
Turaki ya ce idan mutum ya mayar da ƙuri’arsa wani abu da za a iya saya da kuɗi ko kayan abinci, zai iya rage ikonsa na neman ingantaccen shugabanci daga waɗanda ya zaɓa.
Ya ƙara da cewa matasa da sauran ’yan Nijeriya ya kamata su mai da hankali kan irin dokokin da ake samarwa a majalisun dokoki da kuma yadda waɗannan dokoki ke shafar rayuwarsu.
A nasa ɓangaren, tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na Labour Party a zaɓen 2023, Datti Baba-Ahmed, wanda shi ma ya halarci taron, ya yi magana kan matsayin majalisar dattawa da kuma yadda yake ganin tsoma bakin bangaren zartarwa ke shafar ikonta.
Baba-Ahmed ya ce akwai buƙatar majalisar dattawa ta ƙara kare ’yancinta, tare da tabbatar da cewa wakilai na fifita muradun al’ummar da suka zaɓe su.
Ya kuma yi tambaya kan ko ’yan majalisar kasa suna wakiltar shugaban ƙasa da bangaren zartarwa ne, ko kuma mutanen da suka zaɓe su.
Sai dai Turaki ya bayyana rashin amincewarsa da wasu daga cikin bayanan Baba-Ahmed, yana mai cewa bai kamata a mayar da hankali kawai kan ko majalisar dattawa ta yanzu ta yi kama da ta baya ba.
Turaki ya ce abin da ya fi muhimmanci shi ne a tabbatar da cewa an zaɓi ’yan majalisa masu inganci waɗanda za su samar da dokoki da za su taimaka wajen magance matsalolin da ’yan Nijeriya ke fuskanta.
Ya ce bai kamata a duba yawan dokokin da majalisa ta samar kawai ba, sai dai a tambayi ko dokokin suna da amfani ga al’umma da kuma ko za su taimaka wajen magance matsalolin yunwa, rashin aikin yi, talauci da rashin tsaro.
Turaki ya kuma soki duk wata manufar da zai ce tana ƙara wa ’yan Nijeriya nauyi, yana mai cewa ya kamata ’yan majalisa su yi la’akari da tasirin dokoki kan rayuwar jama’a.
Ya yi nuni da batun haraji a matsayin ɗaya daga cikin abubuwan da ya kamata a yi taka-tsantsan wajen duba tasirinsu ga ’yan ƙasa, musamman idan manufofin gwamnati na iya ƙara wa jama’a nauyi.
A cewarsa, manufar wakilcin jama’a ba wai samar da dokoki kawai ba ce, sai dai tabbatar da cewa dokokin suna ƙara inganta rayuwar ’yan Nijeriya da kuma taimakawa wajen magance manyan matsalolin ƙasar.
