Babbar Kotun Zimbabwe ta wanke fitacciyar ‘yar jarida Faith Zaba daga zargin da ake yi mata, bayan ta shafe kusan shekara guda tana fuskantar shari’a kan wani rubutu na barkwanci da ya soki Shugaba Emmerson Mnangagwa, kamar yadda lauyoyinta suka bayyana a ranar Litinin.
An kama Faith Zaba, wadda ita ce editan jaridar Zimbabwe Independent, a watan Yulin 2025 bayan ta wallafa wata makala mai taken “Lokacin da ka zama mai iko da kasar” a sashen barkwanci na jaridar.
Masu gabatar da ƙara sun tuhumi Zaba da laifin cin mutunci da ƙasƙantar da girman Shugaba Mnangagwa, suna zargin cewa manufar makalar ita ce tayar da ƙiyayya da adawa ga shugaban mai shekaru 83 a duniya.
