DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeSiyasaKotu ta umurci a tsare Sowore a gidan gyaran hali na Kuje

Kotu ta umurci a tsare Sowore a gidan gyaran hali na Kuje

Kotun Tarayya da ke Abuja, ƙarƙashin Mai Shari’a Muhammad Umar, ta bayar da umarnin a tsare ɗan gwagwarmaya a Nijeriya Omoyele Sowore a gidan gyaran hali na Kuje.

Kotun ta ce Sowore zai ci gaba da zama a tsare har sai an saurari buƙatar da lauyansa ya shigar domin soke umarnin da ya janye belinsa da kuma sammacin kama shi.

Gidan talabijin na TVC ya ruwaito a zaman kotun da ya gabata, Sowore bai halarta ba, lamarin da ya sa masu gabatar da ƙara suka nemi a soke belinsa, suna zarginsa da ƙoƙarin jinkirta shari’ar. Duk da cewa ya aika wasiƙar neman a ɗage zaman, bai bayyana dalilin rashin zuwansa ba.

A zaman ranar Litinin, Sowore ya halarci kotun tare da sabon lauyansa, Olumide Fusika.

Haka kuma, Mai Shari’a Umar ya yi watsi da wata buƙata da Sowore ya gabatar na neman shari’ar ta koma hannun wani alƙali saboda zargin son kai.

An ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 24 ga Yuni, 2026, domin sauraron buƙatar da ke neman a dawo masa da beli.

Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS ce ke tuhumar Sowore bisa zargin wallafa saƙonnin da suka ƙunshi bayanan ƙarya a kan Shugaba Bola Ahmed Tinubu a shafukansa na X da Facebook.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata