DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeKetareKotu a Zimbabwe ta wanke Ƴar jarida daga zargin cin zarafin Shugaban...

Kotu a Zimbabwe ta wanke Ƴar jarida daga zargin cin zarafin Shugaban Ƙasar

Babbar Kotun Zimbabwe ta wanke fitacciyar ‘yar jarida Faith Zaba daga zargin da ake yi mata, bayan ta shafe kusan shekara guda tana fuskantar shari’a kan wani rubutu na barkwanci da ya soki Shugaba Emmerson Mnangagwa, kamar yadda lauyoyinta suka bayyana a ranar Litinin.

An kama Faith Zaba, wadda ita ce editan jaridar Zimbabwe Independent, a watan Yulin 2025 bayan ta wallafa wata makala mai taken “Lokacin da ka zama mai iko da kasar” a sashen barkwanci na jaridar.

Masu gabatar da ƙara sun tuhumi Zaba da laifin cin mutunci da ƙasƙantar da girman Shugaba Mnangagwa, suna zargin cewa manufar makalar ita ce tayar da ƙiyayya da adawa ga shugaban mai shekaru 83 a duniya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata