DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, October 14, 2026
HomeSiyasaKotu ta bayar da belin Bello Bodejo kan kuɗi Naira biliyan 2

Kotu ta bayar da belin Bello Bodejo kan kuɗi Naira biliyan 2

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belin Shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta Nijeriya, Bello Bodejo, kan kuɗin Naira biliyan biyu, tare da sharadin gabatar da mutane biyu da za su tsaya masa.

Gidan talabijin na TVC ya ruwaito cewa mai shari’a Inyang Ekwo ya bayyana cewa dole ne masu tsayawa belin su kasance mutane masu mutunci da amana.

Haka kuma, ya ce ɗaya daga cikinsu wajibi ne ya mallaki fili a yankin Abuja Municipal Area Council, domin tabbatar da cika sharuɗɗan belin.

Kotun ta kuma umarci cewa ɗaya daga cikin masu tsayawa belin ya gabatar da takardun shaidar biyan haraji na shekarun 2023, 2024 da 2025.

Bugu da ƙari, mai shari’a Ekwo ya umurci Magatakardar kotun ta tantance dukkan takardu da bayanan masu belin kafin a tabbatar da cewa an cika dukkan sharuɗɗan da aka gindaya domin sakin wanda ake tuhuma.

Har ila yau, kotun ta ba da umarnin Bello Bodejo ya miƙa fasfo ɗinsa na tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje ga kotu.

Sannan ta umurci Magatakardar kotun ta sanar da hukumar kula da shige da fice ta Nijeriya game da riƙe fasfon.

Kotun ta kuma hana Bello Bodejo yin tafiya zuwa ƙasashen waje ko fita daga yankin ikon kotun ba tare da izinin kotu ba.

Wannan mataki na daga cikin sharuɗɗan da aka ɗaura masa yayin da ake ci gaba da sauraron shari’ar.

Daga ƙarshe, mai shari’a Inyang Ekwo ya ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranakun 5, 6 da 7 ga Oktoban shekarar 2026.

Hukumar EFCC ce ta gurfanar da Bello Bodejo a ranar 9 ga Yulin 2026 bisa tuhume-tuhume guda 12 da suka shafi zargin halasta kuɗaɗen haram kimanin dala miliyan 2.33 na Amurka.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata