DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Thursday, May 14, 2026
HomeSiyasaKotu ta dage shari’ar shugabancin ADC ba tare da saka rana ba

Kotu ta dage shari’ar shugabancin ADC ba tare da saka rana ba

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sake dage shari’ar da Nafiu Bala Gombe, ya shigar kan rikicin shugabancin jam’iyyar ƙarƙashin tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark.

Mai shari’a Emeka Nwite ne ya ɗage shari’ar ba tare da sanya ranar ci gaba ba bayan mai ƙarar ya sanar da kotu cewa ya nemi a mayar da shari’ar hannun wani alkali daban.

Shari’ar mai lamba FHC/ABJ/CS/1819/2025 ta ƙara haddasa rikicin shugabanci a ADC bayan bayyanar David Mark da tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola, a matsayin shugabannin jam’iyyar.

Lauyan mai ƙarar, Luka Musa Haruna, ya shaida wa kotu cewa Kotun Ƙoli ta yi watsi da ƙarar ɗaukaka ƙara da David Mark ya shigar tun farko, tana mai cewa ba ta da tushe.

Ya kuma ce Kotun Ƙoli ta soke umarnin Kotun Ɗaukaka Ƙara da ya dakatar da sauraron shari’ar.

Sai dai lauyan ya bayyana cewa sun aika wasiƙa ga Alkalin Alƙalan Babbar Kotun Tarayya ranar 4 ga Mayun 2026 domin neman a sauya alkalin da ke sauraron shari’ar.

Lauyoyin waɗanda ake ƙara sun yi adawa da buƙatar, suna zargin mai ƙarar da ƙoƙarin hana a ci gaba da sauraron shari’ar cikin gaggawa kamar yadda kotu ta umarta.

Lauyan David Mark, Sulaiman Usman, ya bayyana matakin a matsayin “nemo kotun da za ta dace da ra’ayin mutane.”

A hukuncinsa, Mai shari’a Nwite ya ce kotu ba za ta iya ɗaukar mataki kan wasiƙar ba tare da sauraron dukkan ɓangarorin shari’ar ba.

Daga nan ne ya dage shari’ar ba tare da sanya ranar ci gaba ba domin a jira matakin da Alkalin Alƙalan Babbar Kotun Tarayya zai ɗauka.

Nafiu Bala Gombe na neman kotu ta hana David Mark da Rauf Aregbesola ci gaba da bayyana kansu a matsayin shugabannin ADC, yana mai cewa tsarin bayyanarsu ya saɓa wa kundin tsarin jam’iyyar da dokar zaɓe.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata