Sanatan da ke wakiltar Bauchi ta Tsakiya, Abdul Ahmed Ningi, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP bayan fiye da shekara 20 yana cikinta.
Ningi ya bayyana hakan ne a cikin wasiƙar murabus da ya aikawa shugaban PDP na mazabar Ningi da ke ƙaramar hukumar Ningi a Jihar Bauchi.
Daily Trust ta ruwaito cewa sanatan ya ce ya ɗauki matakin ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki da magoya bayansa.
Ningi wanda ya shiga PDP tun shekarar 1998, ya taba zama ɗan majalisar wakilai na wa’adi biyu da kuma sanata na wa’adi biyu.
Ya bayyana PDP a matsayin jam’iyyar da ta taɓa kasancewa mafi girma a Afirka mai cike da manufofi da haɗin kai da ƙimar dimokuraɗiyya.
Sai dai ya ce rikicin shugabanci da rarrabuwar kawuna da sabanin ra’ayi a cikin jam’iyyar sun raunana tsarin PDP.
A cewarsa, “Abin damuwa ne yadda wannan babbar jam’iyya mai ƙarfi ta zama ƙungiya mai fama da rikicin shugabanci da son rai na ɓangarori.”
Sanatan ya ce ficewar daga PDP na daga cikin mafi wahalar shawarar siyasa da ya taɓa ɗauka a rayuwarsa.
Ya kuma gode wa shugabannin jam’iyyar a matakai daban-daban bisa goyon bayan da suka ba shi tsawon shekarun da ya yi a PDP.
