DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, July 8, 2026
HomeSiyasaKotun Ɗaukaka Ƙara ta soke amincewa da kwamitin riƙon ƙwarya na PDP...

Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke amincewa da kwamitin riƙon ƙwarya na PDP ɓangaren Wike

Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta soke wasu muhimman sassa na hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta amince da kwamitin riƙon ƙwarya na wani ɓangare na jam’iyyar PDP a matsayin halastaccen shugabancin jam’iyyar.

A hukuncin da Mai Shari’a Uchechukwu Onyemenam ta yanke, kotun ta ce Babbar Kotun Tarayya da ke Ibadan ta bayar da hukuncin da ya wuce abin da ɓangarorin da ke ƙara suka nema a gabanta.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Mai Shari’a Uche Agomoh ta Babbar Kotun Tarayya ta amince da kwamitin riƙon ƙwarya ƙarƙashin jagorancin Abdurahman Mohammed da Samuel Anyanwu a watan Janairu, amma Kotun Ɗaukaka Ƙara ta ce babu wani daga cikin masu shigar da ƙarar da ya nemi a yi irin wannan hukunci.

Kotun ta kuma bayyana cewa hujjar da Babbar Kotun Tarayya ta dogara da ita wajen amincewa da kwamitin ta riga ta rushe bayan hukuncin Kotun Ƙoli da ya soke babban taron PDP da aka gudanar a Ibadan a ranakun 15 da 16 ga Nuwamban 2025.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata