Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na Nijeriya, Mohammed Idris, ya buƙaci malaman addini su guji gabatar da matsalolin tsaro da ƙasar ke fuskanta a matsayin yaƙin addini, yana mai gargadin cewa irin wannan salo na iya kawo cikas ga haɗin kan ƙasa gabanin babban zaɓen 2027.
Idris ya kuma yi kira ga malaman Kirista da su yi amfani da tasirinsu wajen yaɗa gaskiya, zaman lafiya, kishin ƙasa da haƙuri, yana mai jaddada cewa babu wani ɗan Nijeriya da ya kamata a kai wa hari ko nuna masa wariya saboda addininsa.
Ministan ya yi wannan kiran ne a cikin jawabin da ya gabatar a wajen rufe taron Synod na 2026 na Charismatic Bishops Conference of Nigeria da International Communion of Charismatic Archbishops, Bishops and Apostles’, wanda aka gudanar a Abuja ranar Laraba, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Da yake magana kan ’yancin addini da tsaron ƙasa, Idris ya ce gwamnatin tarayya na ci gaba da jajircewa wajen kare haƙƙin ’yan Nijeriya da kundin tsarin mulki ya ba su na yin addininsu cikin ’yanci.
Ministan ya ce gwamnatin Tinubu ta ƙarfafa tattara bayanan sirri, haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da ayyukan sojoji, tare da faɗaɗa haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa kan harkokin tsaro.
Idris ya ce malaman addini na da muhimmiyar rawar da za su taka wajen samar da daidaito tsakanin ra’ayoyin jama’a, saboda irin tasirin da suke da shi a kan miliyoyin ’yan Nijeriya.
