DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Thursday, September 24, 2026
HomeLabaraiKungiyar manoma ta bukaci a samar da tsaro don abinci ya wadata...

Kungiyar manoma ta bukaci a samar da tsaro don abinci ya wadata a Nijeriya

Kungiyar Manoman ‘Cocoa’ da Ayaba ta Nijeriya (CPFAN) ta bukaci gwamnatoci a kowane mataki da su tura masu gadin dazuka zuwa yankunan da ake noma, tana mai cewa tabbatar da tsaron manoma na da matukar muhimmanci wajen cimma bukatar wadatar abinci a kasar.

An yi wannan kira ne a wani shirin hadin gwiwa tsakanin CPFAN da kamfanin ‘Green World Natural Solutions’, wanda aka shirya domin wayar da kan manoma kan amfani da sabbin kayayyaki da fasahohin zamani a harkar noma.

Da yake jawabi a taron, mataimakin shugaban CPFAN na shiyyar Kudu maso Gabas, Samuel Dickson, wanda ya wakilci shugaban kungiyar na kasa, Ayodele Ojo, ya bayyana damuwa kan karuwar matsalolin rashin tsaro da manoma ke fuskanta a sassan Nijeriya.

A cewarsa, manoma da dama na ci gaba da yin watsi da gonakinsu saboda tsoron hare-haren masu aikata laifuka da ke fakewa a cikin dazuka, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Dickson ya bukaci gwamnati da ta tura masu gadin dazuka zuwa cikin dazukan da manoma ke aiki, maimakon a jibge su a manyan hanyoyi da tituna.

Jagoran manoman ya ce hare-haren mamaye gonaki, lalata amfanin gona, satar kayan amfanin gona, garkuwa da mutane da sauran ayyukan laifi sun zama babbar barazana ga yawan amfanin gona da kuma zuba jari a fannin noma.

A cewarsa, rashin tsaro ya sa manoma da dama ba sa iya fadada gonakinsu, lamarin da ke barazana ga kokarin Nijeriya na samar da wadataccen abinci ga al’ummarta.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata