DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeLabaraiKowa na da rawar takawa wajen magance matsalar tsaro a Nijeriya -...

Kowa na da rawar takawa wajen magance matsalar tsaro a Nijeriya – Abdulsalami Abubakar

Tsohon shugaban mulkin soja na Nijeriya, Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya), ya bukaci ‘yan Nijeriya da su hada kai wajen yakar matsalar tsaro, yana mai cewa shawo kan ta’addanci da sauran ayyukan laifi na bukatar hadin gwiwar al’umma, jami’an tsaro da kuma gwamnatoci a kowane mataki.

A cikin wata sanarwa da ya fitar domin bikin cika shekaru 84 da haihuwarsa, Abdulsalami ya nuna damuwa kan yadda matsalar tsaro ke kara ta’azzara a kasar, yana mai jaddada cewa kowane dan Nijeriya yana da rawar da zai taka wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Ya ce mutuwar Manjo Janar Abubakar Rabe (mai ritaya) da sauran mutane da dama sakamakon rashin tsaro, na nuna bukatar gaggauta daukar matakan hadin gwiwa domin magance matsalar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Tsohon shugaban ya ce saboda shekarun da ya kwashe yana aiki a rundunar sojin Nijeriya, ciki har da shiga yakin basasar Nijeriya da kuma ayyukan wanzar da zaman lafiya a kasashen waje, ya fahimci irin sadaukarwar da ake bukata wajen kare kasa.

Ya amince cewa kasashe da dama na fuskantar kalubalen tattalin arziki da na tsaro, amma ya bukaci ‘yan Nijeriya da su ci gaba da mara baya ga duk wani yunkuri na tabbatar da doka da oda.

Abdulsalami ya dora alhakin kara tsananta matsalar tsaro kan siyasantar da batutuwan ta, yana mai gargadin cewa rarrabuwar kawuna da son rai sun raunana kokarin kamo bakin zaren.

Har ila yau, ya nuna damuwa kan yaduwar bayanan karya da rahotannin bogi a kafafen sada zumunta, yana mai cewa hakan na taimakawa ‘yan ta’adda da sauran kungiyoyin masu aikata laifuka wajen cimma manufofinsu.

Ya bukaci ‘yan Nijeriya da su ajiye bambance-bambancen kabila, addini da siyasa, su hada kai wajen yakar masu haddasa tashin hankali da rashin zaman lafiya, yana mai cewa masu aikata laifuka ba sa nuna bambanci kan asali ko akida.

Haka kuma ya karfafa gwiwar jami’an rundunar soji da sauran hukumomin tsaro da su ci gaba da gudanar da ayyukansu cikin jajircewa duk da kalubalen da suke fuskanta, sannan ya bukaci mahukunta su ci gaba da daukar matakan kawo karshen rashin tsaro da hana kara asarar rayuka.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata