DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, May 13, 2026
HomeKetareMainoo ya tsawaita kwantaraginsa da Man United zuwa 2031

Mainoo ya tsawaita kwantaraginsa da Man United zuwa 2031

Dan wasan tsakiya Kobbie Mainoo ya rattaba hannu kan sabon kwantiragi da Manchester United wanda zai rike shi a kungiyar har zuwa shekarar 2031, lamarin da ya kawo karshen jita-jitar da ake yi kan makomarsa.

Mainoo mai shekaru 21, wanda ya shiga makarantar horas da ‘yan wasan kungiyar tun 2014, ya riga ya buga wasanni 98, inda ya ci kwallo mai muhimmanci a wasan karshe na FA Cup na 2024, sannan ya wakilci Ingila a wasan karshe na UEFA Euro 2024.

A cikin kalamansa, Mainoo ya ce Manchester United gida ne a gare shi, yana mai cewa kungiyar na da matukar muhimmanci ga iyalinsa, kuma ya taso yana ganin irin tasirin da take da shi.

Shi kuma daraktan harkokin kwallon kafa na kungiyar, Jason Wilcox, ya yaba da Mainoo, yana mai cewa yana daga cikin matasan ‘yan wasa mafi hazaka a duniya.

Ya ce kwarewarsa, jajircewarsa da kuma halin tawali’u na sa ya zama abin koyi ga matasa, tare da bayyana cewa kungiyar na da yakinin zai zama daya daga cikin fitattun ‘yan wasa a duniya nan gaba, kuma zai taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa Manchester United wajen fafutukar lashe manyan kofuna.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata