DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeLabaraiMajalisar dokokin Kano ta amince da kayyade kudin makarantu masu zaman kansu

Majalisar dokokin Kano ta amince da kayyade kudin makarantu masu zaman kansu

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da kudirin dokar da zai kayyade kudaden makarantu masu zaman kansu tare da dakile karin kudin makaranta ba bisa ka’ida ba.

Kudirin gyaran dokar hukumar kula da makarantu masu zaman kansu da na sa-kai ta Kano na shekarar 2026 ya samu amincewa bayan karatu na uku a zaman majalisar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sabuwar dokar ta tanadi cewa duk wata makaranta mai zaman kanta dole ne ta tuntubi kungiyar iyaye da malamai (PTA) kafin ta kara kudin makaranta, kuma karin ba zai wuce kashi 10 cikin 100 ba.

Haka kuma, kudirin ya tanadi cewa dole ne sakataren zartarwa na hukumar kula da makarantu masu zaman kansu ya kasance gogaggen masani a fannin ilimi, wanda ya kai aƙalla mataki na 14 a aikin gwamnati kafin ya yi ritaya ko ya bar aiki.

Dokar ta kuma haramta wa makarantu masu zaman kansu karbar fiye da kashi 10 cikin 100 a kan kudin rajistar jarabawar hukumomin WAEC, NECO da NABTEB da suka kayyade.

Bugu da kari, an rage kudin harajin da makarantu ke biya wa hukumar daga kashi 15 cikin 100 zuwa kashi biyar cikin 100.

Majalisar ta bayyana cewa wadannan gyare-gyare na daga cikin matakan da ake dauka domin inganta tsarin gudanar da makarantu masu zaman kansu da kuma kara ingancin ilimi a fadin jihar Kano.

Yanzu haka kudirin na jiran sahalewar Gwamna Abba Kabir Yusuf kafin ya zama doka.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata