Shugaban kasar Myanmar, Min Aung Hlaing, ya yi afuwa ga fursunoni sama da 4,000 a wani mataki da aka dauka a matsayin wani bangare na bikin sabuwar shekarar gargajiya ta kasar.
Rahotanni sun nuna cewa wannan afuwa ta shafi kimanin mutane 4,335, ciki har da wasu baki ‘yan kasashen waje kusan 179 da ake sa ran za a mayar da su kasashensu, kamar yadda kafar yada labarai ta Aljazeera ta ruwaito.
Daga cikin wadanda aka saki akwai tsohon shugaban kasar, Win Myint, wanda aka kama tun bayan juyin mulkin soja na shekarar 2021.
Sai dai duk da wannan mataki, tsohuwar shugabar kasar Aung San Suu Kyi ba a sake ta gaba daya ba, sai dai an rage mata hukuncin daurin da take yi.
Wannan mataki na afuwa na zuwa ne bayan sabon shugaban ya hau mulki a watan Afrilun 2026, inda ya bayyana cewa yana son samar da hadin kai da kwanciyar hankali a kasar da ke fama da rikici tun bayan juyin mulkin soja.
Sai dai kungiyoyin kare hakkin bil’adama na ci gaba da nuna damuwa, inda suka ce har yanzu dubban mutane na tsare bisa zarge-zarge irin na siyasa tun bayan juyin mulkin da ya faru a 2021, lamarin da ke ci gaba da tayar da kura a kasar.
