DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, April 17, 2026
HomeSiyasaKo da magudi, Tinubu ba zai iya cin zaben 2027 ba –...

Ko da magudi, Tinubu ba zai iya cin zaben 2027 ba – Amaechi

Tsohon Gwamnan jihar Rivers kuma tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa ‘yan Nijeriya da dama na jiran zaben 2027 domin kada kuri’a su fitar da shugaba Bola Tinubu daga mulki.

Amaechi ya yi wannan furuci ne yayin wata hira a gidan Talabijin na Channels, inda ya ce halin da tattalin arzikin kasar ke ciki ya kara tsananta wahalhalu ga jama’a.

A cewarsa, rayuwa ta yi tsada sosai, inda ya bayyana cewa mutane na fama da rashin kudin sayen abinci, man fetur da kuma tsadar sufuri, yana mai cewa “kowa na cikin wahala.”

Ya kuma soki yadda siyasar kabilanci da addini ke tasiri a zabukan Nijeriya, yana mai cewa irin wadannan abubuwa ne suka taimaka wajen kawo halin da kasar ke ciki a yanzu.

Amaechi ya zargi gwamnati da kokarin raunana jam’iyyun adawa kafin zaben 2027, tare da kira da a bar hukumomi kamar INEC da bangaren shari’a su yi aikinsu cikin ‘yanci.

Ya kara da cewa idan aka gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci, yana da yakinin cewa shugaba Tinubu ba zai yi nasara ba, musamman idan ‘yan adawa suka hada kai.

Sai dai a nasa bangaren, shugaba Tinubu ya yi watsi da irin wadannan kalamai na ‘yan adawa, yana mai cewa ba zai bari suka dauke hankalinsa daga kokarin magance matsalolin Nijeriya ba, tare da jaddada cewa zai ci gaba da gudanar da mulki yadda ya kamata.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata