Wasu matasa a yankin Kwanar Ungogo da ke Jihar Kano sun fara kasuwancin bayar da “power bank” haya domin taimaka wa jama’a wajen cajin waya sakamakon matsalar rashin wutar lantarki da ake fama da ita.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, matasan na gudanar da aikin ne tare da kamfanin Mopo Company, inda ake bayar da “power bank” kan kuɗi N300 na tsawon awa 24, wanda zai iya cajin waya sau huɗu zuwa biyar.
DCL Hausa ta ruwaito cewa kowanne daga cikin wakilan kamfanin na da sama da “power bank” 70, yayin da ake amfani da manhajar waya wajen rajistar kwastomomi da kunna na’urar kafin ta yi aiki.
Ɗaya daga cikin wakilan, Mahmud Sulaiman Bawa, ya ce kafin shiga aikin yana sayar da lemo ne a Kwanar Ungogo, amma yanzu kasuwancin ya zama hanyar samun kuɗaɗen shiga tare da koyon amfani da fasahar zamani.
Mahmud ya ce mutane da dama sun rungumi tsarin saboda yana rage haɗarin satar waya a wuraren caji, yayin da kwastomomi daga yankunan Dawanau da Rijiyar Lemo ke zuwa domin karɓar na’urorin.
Wasu daga cikin masu amfani da tsarin sun ce yana taimaka musu sosai musamman a lokacin rashin wuta. Ismail Abdulkadir ya ce yana iya cajin wayarsa sau biyar cikin sauƙi kafin mayar da “power bank” ɗin.
Matasan sun ce aikin ya kuma koya musu dabarun kasuwancin zamani, amfani da tsarin biyan kuɗi ta intanet da hulɗa da kwastomomi, tare da ƙarfafa musu guiwar rungumar sababbin hanyoyin sana’a.
