Tsohon Babban Daraktan kamfanin man fetur a Nijeriya NNPCL, Mele Kyari, ya bayyana matakin da Majalisar dattawa ta dauka na fitar sanarwar nemanshi ruwa a jallo a matsayin abin mamaki matuka, yana mai cewa tun tuni ya sanar da kwamitin cewa yana jinya a wata kasa da ke wajen Nijeriya.
Kyari ya bayyana hakan ne a wata wasika da ya aikewa shugaban kwamitin majalisar dattawa bayan majalisar ta ba da umarnin kama shi sakamakon rashin halartar zaman binciken da ake yi kan wasu harkokin kudaden NNPCL.
A cewarsa, tun ranar 11 ga Mayu, 2026 ya rubuta wa kwamitin yana sanar da su cewa yana karbar magani a wata kasa da ke wajen Nijeriya, tare da bayyana shirinsa na amsa gayyatar da zarar ya dawo gida.
